1 John 4

Gwada Ruhohi

1Abokaina ƙaunatattu, kada ku gaskata kowane ruhu, sai dai ku gwada ruhohi don ku ga ko daga Allah ne, domin annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya. 2Ga yadda za ku gane Ruhun Allah: Duk ruhun da ya yarda cewa Yesu Kiristi ya zo cikin jiki, to, daga Allah yake, 3amma duk ruhun da bai yarda da Yesu ba, ba daga Allah ba ne. Ruhun magabcin Kiristi ne, wanda kuka ji yana zuwa, har ma ya riga ya shigo duniya.

4Ku, ʼyaʼyana ƙaunatattu, ku daga Allah ne kun kuma yi nasara a kansu, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma. 5Su daga duniya ne saboda haka suke magana yadda duniya take ganin abubuwa, duniya kuwa tana sauraronsu. 6Mu daga Allah ne, kuma duk wanda ya san Allah yakan saurare mu. Amma duk wanda ba daga Allah ba, ba ya sauraronmu. Ta haka ne muke gane Ruhun gaskiya, da kuma ruhun ƙarya.

Ƙaunar Allah da kuma Tamu

7Abokaina ƙaunatattu, mu ƙaunaci juna, domin ƙauna tana zuwa daga Allah ne. Duk mai ƙauna, haifaffe ne na Allah, ya kuma san Allah. 8Duk wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba, domin Allah ƙauna ne. 9Ga yadda Allah ya nuna ƙaunarsa a cikinmu: Ya aiki makaɗaici Ɗansa tilo a duniya domin mu rayu ta wurinsa. 10Wannan ita ce ƙauna: ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya kuma aiko Ɗansa yǎ zama hadaya ta kafara saboda zunubanmu. 11Abokaina ƙaunatattu, da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ya kamata mu ma mu ƙaunaci juna. 12Ba wanda ya taɓa ganin Allah; amma in muna ƙaunar juna, Allah yana raye a cikinmu ƙaunarsa kuwa ta zama cikakkiya a cikinmu ke nan.

13Mun san cewa muna rayuwa a cikinsa shi kuma a cikinmu, domin ya ba mu Ruhunsa. 14Mun gani, mun kuma shaida cewa Uba ya aiko da Ɗansa domin yǎ zama Mai Ceton duniya. 15Duk wanda ya yarda cewa Yesu Ɗan Allah ne, Allah yana raye a cikinsa shi kuma a cikin Allah. 16Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana.

Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa.
17Ta haka, ƙauna ta zama cikakkiya a cikinmu domin mu kasance masu ƙarfin hali a ranar shariʼa, domin a wannan duniya muna kama da shi. 18Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne cikin ƙauna.

19Muna ƙauna domin ya ƙaunace mu da farko. 20Duk wanda ya ce: “Ina ƙaunar Allah,” amma yana ƙin ɗanʼuwansa, maƙaryaci ne. Gama duk wanda ba ya ƙaunar ɗanʼuwansa da ya gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda bai gani ba. 21Ya kuma ba mu wannan umarni: Duk wanda yake ƙaunar Allah dole yǎ ƙaunaci ɗanʼuwansa.

Copyright information for HauSRK